Irm 38:5-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Sarki Zadakiya ya ce, “Ai, ga shi nan a hannunku, gama sarki ba zai yi abin da ba ku so ba.”

6. Sai suka ɗauki Irmiya suka saka shi a rijiyar Malkiya ɗan sarki, wadda take gidan waƙafi. Suka zurara Irmiya a ciki da igiya. Ba ruwa a rijiyar, sai dai lāka, Irmiya ya nutse cikin lākar.

7. Ebed-melek, bābā, mutumin Habasha, wanda yake a gidan sarki, ya ji labari sun saka Irmiya a rijiya. A lokacin nan, sarki yana zaune a Ƙofar Biliyaminu.

8. Sai Ebed-melek ya fita, ya tafi gaban sarki, ya ce masa,

9. “Ya maigirma sarki, waɗannan mutane sun yi mugun abu da suka saka annabi Irmiya cikin fijiya, Zai mutu can da yunwa, gama ba sauran abinci a birnin.”

10. Sa'an nan sarki ya umarci Ebedmelek, mutumin Habasha, ya tafi da mutum talatin su tsamo annabi Irmiya daga cikin rijiyar kafin ya mutu.

11. Sai Ebed-melek ya tafi da mutanen, ya kuma tafi gidan sarki, a ɗakin ajiya, ya kwaso tsummoki da tsofaffin tufafi, ya zurara wa Irmiya a rijiyar.

12. Ebedmelek, mutumin Habasha, ya ce wa Irmiya ya sa tsummokin da tsofaffin tufafin a hammatarsa, ya zarga igiya, Irmiya kuwa ya yi yadda aka ce masa.

13. Suka jawo Irmiya da igiyoyi, suka fito da shi daga rijiya. Irmiya kuwa ya zauna a gidan waƙafi.

Irm 38