22. Ko da za ka yi wanka da sabulunsalo,Ka yi amfani da sabulu mai yawa,Duk da haka zan ga tabbanzunubanka.Ni Ubangiji Allah na faɗa.
23. Ƙaƙa za ka ce ba ka ƙazantar dakanka ba,Ba ka taɓa bin gunkin nan Ba'al ba?Ka duba hanyarka ta zuwa cikinkwari, ka san abin da ka yi.Kana kama da taguwa, mai yawonneman barbara.
24. Kamar jakar jeji kake, wadda takeson barbara,Wadda take busar iska,Sa'ad da take son barbara, wa zai iyahana ta?Jakin da take sonta, ba ya bukatarwahalar da kansaGama a watan barbararta za a sameta.
25. Kai Isra'ila, kada ka bar ƙafafunkaba takalma,Kada kuma ka bar maƙogwaronkaya bushe.Amma ka ce, ‘Wannan ba amfani,Gama na ƙaunaci baƙi, su kuwazan bi.’
26. “Kamar yadda ɓarawo yakan shakunya sa'ad da aka kama shi,Haka nan mutanen Isra'ila za su shakunya,Da su, da sarakunansu, dashugabanninsu,Da firistocinsu, da annabawansu.
27. Waɗanda suka ce wa itace, ‘Kai nemahaifinmu.’Suna kuma ce wa dutse, ‘Kai, kahaife mu.’Gama sun ba ni baya, ba su fuskanceni ba.Amma sa'ad da suke shan wahala,sukan ce,‘Ka zo ka taimake mu.’
28. Ina gumakan da kuka yi wakanku?Bari su tashi in sun iya cetonkulokacin wahalarku.Yahuza, yawan gumakanku sun kaiYawan garuruwanku.
29. Ni Ubangiji, ina tambayarku, ‘Waceƙara kuke da ita game da ni?’Kun yi mini tawaye dukanku.
30. Na hori 'ya'yanku, amma a banza, basu horu ba,Kun kashe annabawanku da takobikamar mayunwacin zaki.
31. Ya ku mutanen zamanin nan, kusaurari maganata.Na zamar wa Isra'ila jeji? Ko ƙasarda take da kurama?Don me fa mutanena suke cewa,‘Mu 'yantattu ne,Ba za mu ƙara zuwa wurinka ba’?
32. Budurwa ta manta da kayankwalliyarta?Ko kuwa amarya ta manta da kayanadonta?Amma mutanena sun manta da nikwanaki ba iyaka.
33. Kun sani sarai yadda za ku yi kufarauci masoya,Har mugayen mata ma, kun koyamusu hanyoyinku.
34. Tufafinku sun ƙasantu da jininmarasa laifi,Waɗanda ba ku same su suna fasagidajenku ba.Amma duk da haka kuna cewa,
35. ‘Ba mu da laifi, hakika kuwa,Ubangiji bai yi fushi da mu ba.’Amma ni Ubangiji zan hukunta ku,Domin kun ce ba ku yi zunubi ba.
36. Me ya sa ba ku da tsayayyiyar zuciya,Sai ku yi nan ku yi can?Masar za ta kunyata ku kamar yaddaAssuriya ta yi.
37. Da hannuwanku a kā za ku komodaga Masar don kunya.Gama waɗanda kuke dogara gare su,ni Ubangiji, na ƙi su,Ba za ku yi arziki tare da su ba.”