Far 41:35-46 Littafi Mai Tsarki (HAU)

35. Bari kuma su tattara dukan abinci a shekarun nan bakwai masu zuwa na albarka, su tsiba a ƙarƙashin ikon Fir'auna saboda abinci cikin birane, su kuma lura da shi.

36. Wannan abinci zai zama ajiya domin ƙasar, kariyar shekaru bakwai na yunwa, waɗanda za a yi cikin ƙasar Masar, domin kada ƙasar ta ƙare saboda yunwar.”

37. Fir'auna da fādawansa duka sun yarda da wannan shawara.

38. Sai Fir'auna ya ce wa fādawansa, “Mā iya samun mutum irin wannan, wanda Ruhun Allah yake cikinsa?”

39. Domin haka Fir'auna ya ce wa Yusufu, “Tun da yake Allah ya nuna maka waɗannan abu duka, ba wani mai basira da hikima kamarka,

40. za ka shugabanci gidana, bisa ga cewarka za a mallaki jama'ata, sai dai da sarauta kaɗai nake gaba da kai.”

41. Fir'auna ya ce wa Yusufu, “Ga shi, na sa ka bisa dukan ƙasar Masar.”

42. Sai Fir'auna ya cire zobensa mai hatimi daga hannunsa ya sa a hannun Yusufu, ya sa masa rigunan lilin masu kyau, ya rataya masa sarƙar zinariya a wuya,

43. ya kuma sa shi ya hau karusarsa ta biyu, suka yi ta shela a gabansa, “Ku ba da hanya.” Ta haka fa ya sa ya zama mai mulki bisa dukan ƙasar Masar.

44. Har yanzu dai Fir'auna ya ce wa Yusufu, “Ni ne Fir'auna, ba mutumin da zai ɗaga hannu ko ƙafa cikin dukan ƙasar Masar idan ba da izninka ba.”

45. Fir'auna kuwa ya sa wa Yusufu suna, Zafenat-faneya. Ya kuma aurar masa da Asenat 'yar Fotifera, firist na On. Yusufu kuwa ya fita rangadin ƙasar Masar.

46. Yusufu yana da shekara talatin lokacin da ya kama aiki a wurin Fir'auna, Sarkin Masar. Yusufu kuwa ya fita daga gaban Fir'auna ya ratsa dukan ƙasar Masar.

Far 41