Ez 3:12-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Sa'an nan Ruhu ya ɗaga ni, sai na ji murya a bayana, kamar babban motsi, tana cewa, “Yabo ga ɗaukakar Ubangiji a kursiyinsa.”

13. Na kuma ji amon fikafikan talikan ne sa'ad da suka taɓa junansu, da kuma amon ƙafafun da suke kusa da talikan, da amon babban motsi.

14. Sai Ruhu ya ɗaga ni, ya kuma tafi da ni, na kuwa tafi da baƙin ciki, ina jin zafi a ruhuna. Ikon Ubangiji yana tare da ni da ƙarfi.

15. Na zo wurin 'yan bautar talala a Telabib, waɗanda suke bakin kogin Kebar. Na zauna tare da su kwana bakwai, ina ta mamaki.

16. A ƙarshen kwana bakwai ɗin, sai Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,

17. “Ɗan mutum, na maishe ka mai tsaron gidan Isra'ila. Sa'ad da ka ji magana daga bakina, sai ka faɗakar da su a madadina.

18. Idan na ce wa mugu, ‘Lalle za ka mutu,’ kai kuwa ba ka faɗakar da shi a kan mugayen ayyukansa don ka ceci ransa ba, wannan mugun mutum zai mutu cikin zunubinsa, amma zan nemi hakkin jininsa a hannunka.

19. Amma idan ka faɗakar da mugu, ya kuwa ƙi barin muguntarsa, zai mutu cikin zunubinsa, kai kam ka kuɓuta.

20. “Idan kuma adali ya bar adalci sa'an nan ya aikata zunubi, ni kuwa na sa abin tuntuɓe a gabansa, zai mutu. Zai mutu saboda zunubinsa domin ba ka faɗakar da shi ba. Ba za a tuna da ayyukansa na adalci waɗanda ya yi ba, amma zan nemi hakkin jininsa a hannunka.

21. Amma idan ka faɗakar da adali, kada ya aikata zunubi, shi kuwa bai aikata zunubi ba, hakika zai rayu domin ya ji faɗakar, kai kuma ka kuɓuta.”

22. Ikon Ubangiji yana tare da ni, Ubangiji kuwa ya ce mini, “Tashi, ka tafi ka tsaya a fili, a can zan yi magana da kai.”

23. Sai na tashi na tafi na tsaya a fili, sai ga ɗaukakar Ubangiji a wurin, a tsaye kamar ɗaukakar da na gani a bakin kogin Kebar. Sai na fāɗi rubda ciki.

24. Ruhu kuwa ya sauko a kaina, ya ta da ni tsaye. Sai ya yi magana da ni, ya ce, “Ka tafi, ka kulle kanka cikin gida.

25. Ya ɗan mutum, za a ɗaure ka da igiyoyi don kada ka tafi cikin jama'a.

26. Ni kuwa zan sa harshenka ya manne wa dasashinka don ka zama bebe, ka kasa tsauta musu, gama su 'yan tawaye ne.

27. Amma sa'ad da na yi magana da kai, zan buɗe bakinka, kai kuwa za ka yi musu magana, ka ce, ‘Ubangiji ya ce, wanda zai ji, to, ya ji, wanda kuma zai ƙi ji, ya ƙi ji,’ gama su 'yan tawaye ne.”

Ez 3