1. Da na duba sararin sama da yake bisa kawunan kerubobi, sai na ga wani abu ya bayyana kamar yakutu. Fasalinsa kamar na kursiyi.
2. Sai Ubangiji ya ce wa mutumin da yake saye da rigar lilin. “Ka shiga ƙarƙashin ƙafafun kerubobin, ka cika tafin hannunka da garwashin wuta wanda yake tsakanin kerubobin, ka watsa bisa kan birnin.”Na kuwa ga ya tafi.
3. Kerubobin kuwa suna tsaye a gefen kudu na Haikalin a sa'ad da mutumin ya shiga, girgije kuma ya cika farfajiyar da take can ciki.
4. Ɗaukakar Ubangiji ta tashi daga kan kerubobin zuwa ƙofar Haikalin. Girgije kuwa ya cika Haikalin, hasken zatin Ubangiji ya cika farfajiyar.
5. Sai aka ji amon fikafikan kerubobin a filin da yake can waje, kamar muryar Allah Maɗaukaki sa'ad da yake magana.
6. Ya kuwa umarci wanda yake saye da lilin ɗin, ya ce, “Ka ɗibi wuta daga ƙarƙashin ƙafafun da suke tsakanin kerubobin.” Sai ya tafi ya tsaya a gefen ƙafar.
7. Kerub kuwa ya miƙa hannunsa daga tsakanin kerubobi zuwa wurin wutar da take tsakanin kerubobin, ya ɗebo wutar, ya zuba a ahannun mutumin da yake saye da rigar lilin. Shi kuwa ya karɓa, ya fita.
8. Kerubobin suna da hannuwa kamar na 'yan adam a ƙarƙashin fikafikansu.
9. Da na duba, sai na ga ƙafa guda huɗu kusa da kerubobin. Kowane kerub yana da ƙafa ɗaya kusa da shi. Ƙafafun suna ƙyalli kamar wani dutse mai daraja.
10. Dukansu kuwa kamanninsu ɗaya, kamar ƙafa a cikin ƙafa.