6. Ubangiji ya ce,“Mutanen Isra'ila sun ci gaba da yinzunubi.Hakika, zan hukunta su,Don sun sayar da salihai waɗandasuka kāsa biyan bashinsu.Sun kuma sayar da matalautaWaɗanda bashinsu bai kai ko kuɗinbi-shanu ba.
7. Sun tattake marasa ƙarfi dakāsassu,Suna tunkuɗe matalauta su wuce.Tsofaffi da samari sukan tafi wurinkaruwan Haikali.Ta haka suke ɓata sunana maitsarki.
8. A duk wuraren sujadarsu sukankwantaA bisa tufafin da suka karɓe jingina.A cikin Haikalin Allahnsu, sukan sharuwan inabiDa suka karɓo daga wurin waɗandasuke bi bashi.