18. Yehowash Sarkin Isra'ila fa ya aika wa Amaziya Sarkin Yahuza, da amsa ya ce, “Wata ƙaya ce a Lebanon, ta aika wa itacen al'ul na Lebanon cewa, ‘Ka ba ɗana 'yarka aure,’ sai wani naman jeji na Lebanon da yake wucewa, ya tattake ƙayar.
19. Ka ce, ga shi, ka ci Edom, zuciyarka ta sa ka fāriya. Amma yanzu sai ka yi zamanka, don me ka tsokano wahalar da za ta kā da kai, da kai da Yahuza tare da kai?”
20. Amma Amaziya ya ƙi ji, gama al'amarin daga wurin Allah yake, domin ya bashe su a hannun maƙiyansu, saboda sun koma ga gumakan Edom.
21. Sarkin Isra'ila kuwa ya haura, da shi da Amaziya Sarkin Yahuza, suka gabza da juna fuska da fuska a Bet-shemesh, wadda take a ƙasar Yahuza.
22. Sai Isra'ila ya runtumi Yahuza, kowane mutum ya gudu zuwa gidansa.
23. Yehowash Sarkin Isra'ila, ya kama Amaziya Sarkin Yahuza ɗan Yowash, wato jikan Ahaziya, a Bet-shemesh, ya kawo shi Urushalima. Ya rushe garun Urushalima har tsawon kamu ɗari huɗu, tun daga Ƙofar Ifraimu har zuwa Ƙofar Kusurwa,
24. sai ya kwashe dukan zinariya da azurfa, da dukan tukwane da tasoshi da aka samu a Haikalin Allah, waɗanda iyalin Obededom suke tsaro, da kaya masu daraja na gidan sarki, da waɗanda aka kamo cikin yaƙi, ya kawo Samariya.
25. Sarki Amaziya ɗan Yowash, Sarkin Yahuza, ya rayu shekara goma sha biyar bayan rasuwar Yehowash ɗan Yehowahaz Sarkin Isra'ila.
26. Sauran ayyukan Amaziya, daga farko har ƙarshe, an rubuta su a littafin sarakunan Yahuza da na Isra'ila.
27. Daga lokacin da Amaziya ya bar bin Ubangiji, sai suka shirya masa maƙarƙashiya a Urushalima, amma ya gudu zuwa Lakish, sai suka sa a bi shi zuwa Lakish, a can suka kashe shi.
28. Sai suka kawo shi a bisa dawakai, suka binne shi tare da kakanninsa a birnin Dawuda.