Yehowash Sarkin Isra'ila, ya kama Amaziya Sarkin Yahuza ɗan Yowash, wato jikan Ahaziya, a Bet-shemesh, ya kawo shi Urushalima. Ya rushe garun Urushalima har tsawon kamu ɗari huɗu, tun daga Ƙofar Ifraimu har zuwa Ƙofar Kusurwa,