13. Amma barorinsa suka je wurinsa, suka ce masa, “Ranka ya daɗe, da a ce annabin ya umarce ka ka yi wani babban abu ne, ashe, da ba ka yi ba, balle wannan, da ya ce ka tafi ka yi wanka, ka tsarkaka?”
14. Sai ya tafi ya yi wanka har sau bakwai a Kogin Urdun bisa ga maganar annabin Allah, sai naman jikinsa ya warke ya zama kamar na ƙaramin yaro, ya tsarkaka.
15. Ya kuwa komo wurin annabi Elisha shi da jama'arsa duka, ya zo ya tsaya a gabansa, ya ce, “Yanzu na sani a duniya duka ba wani Allah banda na Isra'ila, saboda haka, sai ka karɓi kyauta daga wurina.”
16. Amma Elisha ya ce, “Na rantse da Ubangiji, wanda nake bauta masa, ba zan karɓi kome ba.”Ya yi ta roƙonsa ya karɓa, amma ya ƙi.
17. Na'aman kuwa ya ce, “Da yake ka ƙi ka karɓa, ina roƙonka, ka ba baranka labtun alfadari biyu na ƙasa, gama nan gaba baranka ba zai ƙara miƙa hadaya ta ƙonawa ko baiko ga wani gunki ba, sai dai Ubangiji.
18. Sai dai Ubangiji ya gafarta mini lokacin da na bi sarki zuwa cikin haikalin Rimmon, gunkin Suriya, don ya yi sujada. Na gaskata Ubangiji zai gafarta mini.”
19. Elisha kuwa ya ce masa, “Ka sauka lafiya.” Na'aman ya tafi.Amma tun Na'aman bai yi nisa ba,
20. sai Gehazi, baran annabi Elisha, ya ce, “Duba, maigidana ya bar Na'aman Basuriyen nan ya tafi, bai karɓi kome daga cikin abin da ya kawo masa ba. Na rantse da Ubangiji, zan sheƙa a guje, in bi shi, in karɓi wani abu daga gare shi.”
21. Gehazi kuwa ya bi bayan Na'aman.Da Na'aman ya ga wani yana biye da shi a guje, sai ya sauka daga karusarsa, ya juya ya tarye shi, ya ce, “In ce ko lafiya?”
22. Gehazi ya ce, “Lafiya ƙalau, maigidana ne ya aiko ni in faɗa maka, yanzu yanzu waɗansu samari biyu daga ƙungiyar annabawa suka zo wurinsa daga ƙasar tudu ta Ifraimu, yana roƙonka, ka ba ni talanti ɗaya na azurfa da rigunan ado guda biyu in kai masa.”
23. Na'aman kuwa ya ce, “In ka yarda ka karɓi talanti biyu na azurfa.” Ya ƙirga su ya ɗaure kashi biyu, da kuma rigunan ado masu kyau ya ɗora wa barorinsa biyu, ya umarce su su kai wa Gehazi har gida.
24. Sa'ad da Gehazi ya kai tudu, sai ya karɓi kayan daga hannunsu, ya ajiye a gida, sa'an nan ya sallame su, suka tafi.
25. Sai ya shiga, ya tsaya a gaban Elisha, Elisha kuwa ya tambaye shi, “Ina ka tafi, Gehazi?”Sai ya ce, “Ranka ya daɗe ban tafi ko'ina ba.”
26. Amma Elisha ya ce masa, “Ashe, ba ina tare da kai a ruhu ba, sa'ad da mutumin ya juyo daga karusarsa don ya tarye ka? Wannan shi ne lokacin karɓar kuɗi, da riguna, da gonaki na zaitun, da na inabi, da tumaki, da shanu, da barori mata da maza?
27. Saboda haka kuturtar Na'aman za ta kama ka, kai da zuriyarka har abada.”Haka kuwa ya fita a wurinsa kuturu, fari fat kamar auduga.