11. Uriya firist kuwa, ya gina bagaden bisa ga yadda sarki Ahaz ya aika masa daga Dimashƙu. Uriya firist, ya gina bagaden kafin sarki Ahaz ya komo daga Dimashƙu.
12. Da sarki ya komo daga Dimashƙu, ya hango bagaden, sai ya tafi kusa da shi.
13. Sa'an nan ya miƙa hadayarsa ta ƙonawa, da hadayarsa ta gari, da hadayarsa ta sha, ya yayyafa jinin hadayarsa ta salama a bisa bagaden.
14. Sai ya kawar da bagaden tagulla wanda aka keɓe ga Ubangiji, ya sa shi arewacin sabon bagadensa.
15. Sarki Ahaz ya umarci Uriya firist cewa, “Sai ka miƙa hadaya ta ƙonawa ta safe, da hadaya ta gari ta maraice, da hadaya ta ƙonawa ta sarki, da hadayarsa ta gari, da hadaya ta ƙonawa ta dukan jama'ar ƙasar, da hadayarsu ta gari, da hadayarsu ta sha, ka yayyafa dukan jinin hadaya ta ƙonawa, da dukan jinin hadayu a bisa babban bagaden. Amma bagaden tagulla zai zama nawa don yin ibada.”
16. Uriya firist kuwa, ya yi dukan abin da sarki Ahaz ya umarta.
17. Sarki Ahaz kuwa ya yanke sassan dakalan, ya ɗauke daruna da suke bisansu, ya kuma ɗauke kwatarniya da take bisa bijimai na tagulla, ya ajiye kwatarniya a daɓen dutse.
18. Hanyar da aka killace ta Asabar, wadda suka yi a cikin gidan, da ƙofar waje ta shigar sarki, Ahaz ya kawar da su daga Haikalin Ubangiji saboda Sarkin Assuriya.
19. Sauran ayyukan Ahaz waɗanda ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.
20. Ahaz ya mutu, aka binne shi a makabartar kakanninsa a birnin Dawuda. Sai ɗansa, Hezekiya, ya gaji sarautarsa.