2 Sar 13:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A shekara ta ashirin da uku ta sarautar Yowash ɗan Ahaziya Sarkin Yahuza, Yehowahaz ɗan Yehu ya ci sarautar Isra'ila a Samariya. Ya yi mulki shekara goma sha bakwai.

2. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, gama ya aikata irin zunuban Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra'ilawa su yi zunubi. Bai rabu da zunuban Yerobowam ba.

3. Ubangiji kuwa ya husata da jama'ar Isra'ila, sai ya dinga ba da su a hannun Hazayel Sarkin Suriya, da hannun Ben-hadad ɗan Hazayel.

4. Sai Yehowahaz ya roƙi Ubangiji, Ubangiji kuwa ya ji shi, gama ya ga wahalar da Isra'ilawa suke ciki, wato yadda Sarkin Suriya yake musguna musu.

5. Saboda haka Ubangiji ya ba jama'ar Isra'ila maceci, suka kuwa kuɓuta daga ƙangin Suriyawa, suka zauna a gidajensu lafiya kamar dā.

16-17. Sa'an nan ya ce, “Ka buɗe tagar da take wajen gabas.” Sai ya buɗe. Elisha ya kuma ce masa, “Ka ja bakan.” Ya kuwa ja. Sai Elisha ya ɗora hannuwansa a bisa hannuwan sarki. Sa'an nan Elisha ya ce, “Harba.” Sai ya harba. Elisha kuwa ya ce, “Kibiyar Ubangiji ta nasara, kibiyar nasara a kan Suriya. Gama za ka yi yaƙi da Suriyawa a Afek har ka ci su.”

2 Sar 13