2 Sam 24:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji kuwa ya husata da Isra'ilawa. Ya kuwa zuga Dawuda a kansu, ya ce, “Tafi ka ƙidaya jama'ar Isra'ila da ta Yahuza.”

2. Sai sarki ya ce wa Yowab da shugabannin sojojin su tafi cikin dukan kabilan Isra'ila, tun daga Dan har zuwa Biyer-sheba, su ƙidaya mutanen don ya san yawansu.

3. Amma Yowab ya ce wa sarki, “Ubangiji Allahnka ya sa mutanenka su ƙaru har sau ɗari fiye da yadda suke, har ubangijina sarki ya gani da idonsa, amma me ya sa sarki yake so ya yi wannan abu?”

4. Amma maganar sarki ta rinjayi ta Yowab da ta sauran shugabannin sojojin. Yowab kuwa da sauran shugabannin sojojin suka tashi daga gaban sarki suka tafi su ƙidaya mutanen Isra'ila.

5. Suka haye Urdun suka fara daga Arower, da garin da yake tsakiyar kwarin zuwa Gad, har zuwa Yazar.

6. Sa'an nan suka zo Gileyad da Kadesh cikin ƙasar Hittiyawa, daga nan suka tafi Dan-ja'an. Daga Dan-ja'an kuma suka ratsa zuwa Sidon.

7. Suka tafi kagarar Taya da dukan garuruwan Hiwiyawa, da na Ƙan'aniyawa. Daga can suka tafi ƙasar kudu ta Yahuza a Biyer-sheba.

8. Da suka gama ratsa dukan ƙasar, sai suka komo Urushalima bayan wata tara da kwana ashirin.

9. Yowab kuwa ya ba sarki yawan jimillar mutanen da aka samu. A Isra'ila an sami mutanen da suka isa yin yaƙi, su dubu ɗari takwas (800,000). A Yahuza kuwa an sami mutum dubu ɗari biyar (500,000).

10. Bayan da Dawuda ya ƙidaya mutane, sai lamirinsa ya kā da shi, ya ce wa Ubangiji, “Na yi laifi ƙwarai a kan abin da na yi. Ina roƙonka, ya Ubangiji, ka gafarta mini, gama na yi wauta.”

11. Da Dawuda ya tashi da safe, sai Ubangiji ya yi magana da annabi Gad, wato annabin da yake tare da Dawuda, ya ce,

2 Sam 24