2 Sam 2:1-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Bayan wannan sai Dawuda ya roƙi Ubangiji, ya ce, “Ko in haura in mallaki ɗaya daga cikin garuruwan Yahuza?”Ubangiji ya ce masa, “Ka haura.”Dawuda kuma ya ce, “Zuwa wane gari zan haura?”Sai Ubangiji ya ce masa, “Zuwa Hebron.”

2. Dawuda kuwa ya haura zuwa can tare da matansa biyu, wato Ahinowam Bayezreyeliya, da Abigail matar marigayi Nabal Bakarmele.

3. Ya kuma tafi tare da mutanen da suke tare da shi, kowa da iyalinsa. Suka zauna a garuruwan Hebron.

4. Mutanen Yahuza kuwa suka zo, suka naɗa Dawuda da man naɗawa domin ya zama Sarkin Yahuza.Da Dawuda ya ji labari mutanen Yabesh-gileyad, sun binne Saul,

5. sai ya aiki manzanni da saƙo wurin mutanen Yabesh-gileyad ya ce, “Ubangiji ya sa muku albarka da yake kun yi wa Saul, ubangijinku, wannan alheri, har kuka binne shi.

6. Ubangiji ya nuna muku ƙaunarsa da amincinsa. Ni kuwa zan yi muku alheri saboda abin da kuka yi.

7. Yanzu sai ku ƙarfafa, ku yi jaruntaka, gama Saul shugabanku ya rasu, mutanen Yahuza kuwa sun naɗa ni sarkinsu.”

8. Abner kuwa ɗan Ner, sarkin yaƙin Saul, ya tsere da Ish-boshet, ɗan Saul, zuwa Mahanayim.

9. Ya naɗa shi Sarkin Gileyad, da Ashiru, da Yezreyel, da Ifraimu, da ƙasar Biliyaminu, da dukan Isra'ila.

10. Ish-boshet, ɗan Saul, yana da shekara arba'in sa'ad da ya ci sarautar Isra'ila, ya yi shekara biyu yana sarauta. Amma mutanen Yahuza suka bi Dawuda.

11. Dawuda ya yi shekara bakwai da rabi yana sarautar Yahuza a Hebron.

12. Abner, ɗan Ner, tare da fādawan Ish-boshet, ɗan Saul, suka tashi daga Mahanayim zuwa Gibeyon.

13. Sai kuma Yowab, ɗan Zeruya, tare da fādawan Dawuda suka fita suka tafi tarye su a tafkin Gibeyon. Suka zauna, waɗannan a wannan gefe, waɗancan a wancan gefe na tafkin.

2 Sam 2