2 Sam 19:32-43 Littafi Mai Tsarki (HAU)

32. Barzillai kuwa tsoho ne, yana da shekara tamanin. Ya taimaki sarki da abinci sa'ad da sarki yake a Mahanayim, gama shi attajiri ne.

33. Sarki ya ce wa Barzillai, “Ka zo mu tafi tare zuwa Urushalima, ni kuwa zan riƙa biya maka bukata.”

34. Amma Barzillai ya amsa, ya ce, “Shekaruna nawa suka ragu har da zan tafi Urushalima tare da sarki?

35. A yau ina da shekara tamanin cif. Ba zan iya in rarrabe abu mai daɗi da marar daɗi ba. Ba kuma zan iya ɗanɗana daɗin abin da nake ci ko abin da nake sha ba. Ba zan iya jin daɗin muryar mawaƙa ba. Zan zamar maka kaya kurum, ranka ya daɗe.

36. Ban cancanci wannan irin babban lada ba. Zan dai yi maka 'yar rakiya zuwa hayin Urdun.

37. Ina roƙonka ka bar ni in koma domin in rasu a garinmu, kusa da kabarin mahaifina. Amma ga Kimham barana, bari ya tafi tare da kai, ranka ya daɗe. Ka yi masa yadda kake so.”

38. Sarki ya ce, “To, Kimham zai tafi tare da ni, zan kuwa yi masa abin da zai yi maka daɗi. Duk abin da kake so a gare ni, zan yi maka.”

39. Sa'an nan dukan jama'a suka haye Urdun, sarki kuma ya haye. Ya yi bankwana da Barzillai, ya sumbace shi, ya kuma sa masa albarka. Sai Barzillai ya koma gidansa.

40. Sarki kuwa ya yi tafiya zuwa Gilgal. Kimham kuma ya tafi tare da shi. Mutanen Yahuza duka, da rabin mutanen Isra'ila suna tafe tare da sarki.

41. Sai dukan mutanen Isra'ila suka zo wurin sarki, suka ce masa, “Me ya sa mutanen Yahuza 'yan'uwanmu, suka sace ka, suka kawo sarki da iyalinsa a wannan hayin Urdun, tare da dukan mutanensa?”

42. Dukan mutanen Yahuza suka amsa wa mutanen Isra'ila suka ce, “Domin sarki ɗan'uwanmu ne na kusa. Me ya sa kuke fushi a kan wannan al'amari? Me muka ci a jikin sarki, ko kun ji ya ba mu wani abu ne?”

43. Isra'ilawa kuma suka amsa wa mutanen Yahuza, suka ce, “Muna da rabo goma a wurin sarki Dawuda fiye da ku, don me kuka raina mu? Ba mu ne muka fara maganar komowar sarki ba?”Amma maganar mutanen Yahuza ta fi ta mutanen Isra'ila zafi.

2 Sam 19