19. Sa'an nan ya ce mata, “Ko akwai hannun Yowab cikin dukan sha'anin nan naki?”Ita kuwa ta amsa, “Na rantse da kai, ya ubangijina, sarki, ba dama a yi maka ƙumbiya-ƙumbiya. Haka ne, Yowab baranka ne ya sa ni. Shi ya sa dukan waɗannan magana a bakin baranyarka.
20. Yowab baranka ya yi wannan don ya daidaita al'amarin. Amma ubangijina yana da hikima irin ta mala'ikan Allah domin ya san dukan al'amuran da suke a duniya.”
21. Sa'an nan sarki ya ce wa Yowab, “To, na yarda, sai ka tafi ka komo da saurayin nan, Absalom.”
22. Sai Yowab ya rusuna har ƙasa da bangirma, ya yi wa sarki kyakkyawan fata. Ya kuma ce, “Yau na sani na sami tagomashi a wurinka, ya ubangijina, sarki, da yake ka amsa roƙona.”
23. Sa'an nan Yowab ya tashi, ya tafi Geshur, ya komo da Absalom Urushalima.
24. Sarki ya ce a sa shi ya koma gidansa, kada ya zo gabansa. Absalom kuwa ya yi zamansa can gidansa, bai je gaban sarki ba.
25. A cikin Isra'ila duka ba wanda ake yaba kyansa kamar Absalom. Tun daga tafin sawunsa har zuwa bisa kansa ba shi da makusa.
26. Sa'ad da ya yi aski yakan auna nauyin gashin kansa, nauyin yakan kai wajen shekel ɗari biyu. Gama a ƙarshen kowace shekara yake aski, sa'ad da gashin ya yi masa nauyi.
27. Aka haifa wa Absalom 'ya'ya uku maza da 'ya mace guda, sunanta Tamar, ita kuwa kyakkyawa ce.
28. Absalom ya yi shekara biyu cif a Urushalima, amma bai sami izinin ganin sarki ba.
29. Sai Absalom ya aika a kira masa Yowab don ya aike shi wurin sarki, amma Yowab ya ƙi zuwa. Ya kuma sāke aikawa, Yowab kuwa ya ƙi zuwa.
30. Sai ya ce wa barorinsa, “Ga Yowab yana da gonar sha'ir kusa da tawa, ku tafi, ku sa mata wuta.” Barorin Absalom kuwa suka tafi suka sa wa gonar wuta.
31. Yowab kuwa ya tashi ya tafi wurin Absalom har gidansa, ya ce masa, “Don me barorinka suka sa wa gonata wuta?”
32. Absalom ya ce wa Yowab, “Har sau biyu na aika maka domin ka zo in aike ka wurin sarki, ka tambaya mini, ‘Ko me ya sa na komo daga Geshur?’ Da ma ina can har yanzu, ai, da ya fi mini. Yanzu har ni in tafi wurin sarki, idan ina da laifi, to, ya kashe ni.”
33. Sai Yowab ya tafi wurin sarki, ya faɗa masa. Sarki ya sa a kira Absalom. Absalom kuwa ya zo gaban sarki, ya rusuna har ƙasa. Sarki kuwa ya marabce shi, ya yi masa sumba.