1 Tar 18:8-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Dawuda kuma ya kwaso tagulla mai yawan gaske daga Beta da Berotayi, biranen Hadadezer. Da su ne Sulemanu ya yi kwatarniya, da ginshiƙai, da kayayyakin Haikali.

9. Sa'ad da Toyi, Sarkin Hamat, ya ji an ce Dawuda ya riga ya ci nasara a kan sojojin Hadadezer, Sarkin Zoba,

10. sai ya aiki Adoniram ɗansa wurin sarki Dawuda, don ya gaishe shi, ya kuma yabe shi saboda ya yi yaƙi da Hadadezer, har ya ci shi, gama Hadadezer yakan yi yaƙi da Toyi. Adoniram kuwa ya kawo kayayyaki iri iri na zinariya, da na azurfa, da na tagulla.

11. Sarki Dawuda kuwa ya keɓe waɗannan ga Ubangiji, tare da azurfa da zinariya waɗanda ya kwaso daga al'umman da ya ci, wato Edom, da Mowab, da mutanen Ammon, da na Filistiya, da na Amalek.

12. Abishai ɗan Zeruya kuma ya ci nasara a kan Edomawa, mutum dubu goma sha takwas (18,000) a Kwarin Gishiri.

13. Sai ya sa ƙungiyoyin sojoji a Edom, dukan Edomawa kuma suka zama bayin Dawuda. Ubangiji kuwa ya taimaki Dawuda duk inda ya tafi.

14. Da haka Dawuda ya yi mulki bisa dukan Isra'ila. Ya yi wa dukan jama'arsa adalci da gaskiya.

15. Yowab ɗan Zeruya shi ne shugaban sojoji, Yehoshafat ɗan Ahilud shi ne marubuci.

16. Zadok ɗan Ahitub da Ahimelek ɗan Abiyata su ne firistoci, Seraiya kuwa shi ne magatakarda.

17. Benaiya ɗan Yehoyada shi ne shugaban Keretiyawa da Feletiyawa, wato matsara. 'Ya'yan Dawuda, maza, su ne manyan ma'aikata na kusa da shi.

1 Tar 18