Sarki Dawuda kuwa ya keɓe waɗannan ga Ubangiji, tare da azurfa da zinariya waɗanda ya kwaso daga al'umman da ya ci, wato Edom, da Mowab, da mutanen Ammon, da na Filistiya, da na Amalek.