14. Sai shi da Dawuda suka shiga gonar sha'ir ɗin, suka tsaya ciki don su tsare ta. Suka ragargaza Filistiyawa, Ubangiji kuwa ya cece su, ya ba su babbar nasara.
15. Wata rana sai uku daga cikin manyan mutanen nan talatin suka gangara zuwa dutsen Dawuda, a kogon Adullam, sa'ad da rundunar sojojin Filistiyawa suka kafa sansani a kwarin Refayawa.
16. Dawuda yana cikin kagara, sojojin Filistiyawa kuwa suna a Baitalami.
17. Sai Dawuda ya yi marmarin gida, ya ce, “Dā ma wani ya kawo mini ruwa daga rijiyar da take a ƙofar Baitalami in sha!”
18. Sai uku ɗin suka kutsa kai, suka shiga sansanin Filistiyawa, suka ɗebo ruwa daga rijiyar da take a ƙofar Baitalami, suka ɗauka, suka kawo wa Dawuda, Dawuda kuwa bai sha ba, amma ya kwarara ruwan a ƙasa domin sadaka ga Ubangiji.
19. Sa'an nan ya ce, “Allah ya sawwaƙe mini da zan yi wannan abu a gabansa, da zan sha jinin waɗannan da suka sadaukar da rayukansu, gama sai da suka yi kasai da ransu, sa'an nan suka ɗebo ruwan.” Saboda haka bai sha ruwan ba. Manyan jarumawan nan uku ne suka aikata waɗannan abubuwa.
20. Abishai ɗan'uwan Yowab kuwa shi ne shugaban jarumawa talatin ɗin. Ya girgiza mashinsa, ya kashe mutum ɗari uku. Ya yi suna a cikin jarumawan nan talatin.
21. Cikin jarumawa talatin ɗin, shi ya shahara har ya zama shugabansu. Amma duk da haka bai kai ga jarumawan nan uku ba.
22. Benaiya ɗan Yehoyada, ɗan wani jarumi ne daga Kabzeyel, ya yi manyan ayyuka, ya kashe jarumawa biyu na Mowabawa. Sai ya gangara ya kashe zaki a cikin rami a ranar da ake yin dusar ƙanƙara.
23. Sai kuma ya kashe wani dogon Bamasare mai tsayi kamu biyar. Bamasaren yana da māshi mai kama da dirkar masaƙa a hannunsa, amma sai ya gangaro wurinsa da kulki a hannu, ya ƙwace māshin daga hannun Bamasaren, ya kashe shi da shi.
24. Waɗannan abubuwa Benaiya ɗan Yehoyada ya yi su, ya kuwa yi suna kamar manyan jarumawan nan uku.