Sa'an nan ya ce, “Allah ya sawwaƙe mini da zan yi wannan abu a gabansa, da zan sha jinin waɗannan da suka sadaukar da rayukansu, gama sai da suka yi kasai da ransu, sa'an nan suka ɗebo ruwan.” Saboda haka bai sha ruwan ba. Manyan jarumawan nan uku ne suka aikata waɗannan abubuwa.