1 Tar 12:1 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Mutane da yawa suka haɗa kai da Dawuda lokacin da yake a Ziklag, sa'ad da yake a takure saboda Saul ɗan Kish. Su ma suna cikin manyan jarumawan da suka taimake shi yaƙi. Dukansu gwanayen sojoji ne, suna iya su harba kibiya, ko su yi jifa da majajjawa da hannun dama ko da na hagu.

1 Tar 12

1 Tar 12:1-9-13