1 Sam 19:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sai Saul ya yi magana da Jonatan, ɗansa, da dukan fādawansa, cewa yana shiri ya kashe Dawuda. Amma Jonatan ɗan Saul yana jin daɗin Dawuda ƙwarai.

2. Jonatan ya faɗa wa Dawuda ya ce, “Saul, mahaifina, yana so ya kashe ka, domin haka sai ka lura da kanka da safe, ka ɓuya a wani lungu.

3. Ni kuwa zan tafi in tsaya kusa da mahaifina a saura inda ka ɓuya, zan yi masa magana a kanka, abin da ya faru, zan sanar da kai.”

4. Jonatan kuwa ya yabi Dawuda a gaban Saul, ya ce masa, “Kada sarki ya yi wa baransa, Dawuda, laifi, gama shi bai yi maka laifi ba, ayyukansa kuma a gare ka masu kyau ne.

1 Sam 19