20. Lalle hakika, ina gaya muku, za ku yi kuka da kuma gunji, amma duniya za ta yi farin ciki. Za ku yi baƙin ciki, amma baƙin cikinku zai koma farin ciki.
21. Idan mace tana naƙuda takan sha wuya, don lokacin haihuwarta ya yi. Amma da zarar ta haifi jinjirin, ba ta ƙara tunawa da wahalar da ta sha, domin murnar an sami baƙon duniya.
22. Haka ku ma yanzu kuke tare da baƙin ciki, amma zan sāke ganinku, sa'an nan zuciyarku za ta yi fari, ba kuwa mai ɗauke muku farin cikinku.
23. A ran nan, ba za ku yi mini wata tambaya ba. Lalle hakika, ina gaya muku, kome kuka roƙi Uba zai ba ku saboda sunana.
24. Har yanzu dai ba ku roƙi kome da sunana ba. Ku roƙa, za ku samu, domin farin cikinku ya zama cikakke.”
25. “Duk wannan na faɗa muku da misalai ne. Lokaci yana zuwa da ba zan ƙara faɗa muku kome da misalai ba, sai dai in ba ku labarin Uba a sarari.
26. A ran nan za ku yi roƙo da sunana. Ban kuwa ce muku zan roƙar muku Uba ba,
27. domin shi Uban kansa na ƙaunarku, domin kun ƙaunace ni, kun kuma gaskata daga wurin Uban na fito.
28. Daga wurin Uban ne na fito, na shigo duniya, har wa yau kuma zan bar duniya in koma wurin Uba.”
29. Sai almajiransa suka ce, “Yauwa! Yanzu ne fa kake magana a sarari, ba da misali ba!
30. Yanzu ne muka tabbata ka san kome, ba sai wani ya tambaye ka ba. Ta haka muka gaskata daga wurin Allah ka fito.”
31. Yesu ya amsa musu ya ce, “Ashe, yanzu kun gaskata?
32. To, lokaci na zuwa, har ma ya yi, da za a warwatsa ku, kowa yă koma gidansu, ku bar ni ni kaɗai. Duk da haka kuwa ba ni kaɗai nake ba, domin Uba na tare da ni.
33. Na faɗa muku wannan ne domin a gare ni ku sami salama. A duniya kuna shan wuya, amma dai ku yi farin ciki, ai, na yi nasara da duniya.”