Rom 9:4-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Su ne Isra'ilawa. Da zama 'ya'yan Allah, da ganin ɗaukakarsa, da alkawaran nan, da baiwar Shari'a, da ibada, da kuma sauran alkawarai, duk nasu ne.

5. Kakannin kakannin nan kuma nasu ne, Almasihu kuma, ta wurin zamansa mutum, na kabilarsu ne. Yabo yā tabbata ga Allah har abada, shi da yake bisa kome. Amin.

6. Ba cewa Maganar Allah ta fādi ba, don ba duk zuriyar Isra'ila ne suke Isra'ilawa na gaske ba.

7. Ba kuwa duk su ne 'ya'yan Ibrahim ba, wai don suna zuriyarsa. Amma an ce, “Ta wurin Ishaku ne za a lasafta zuriyarka.”

8. Wato, zaman zuriyar Ibrahim, ba shi ne zama 'ya'yan Allah ba, a'a, zuriya ta alkawarin nan su ne ake lasaftawa zuriyar Ibrahim.

9. Alkawarin kuwa shi ne, “Baɗi war haka zan dawo, Saratu kuma za ta haifi ɗa.”

10. Banda haka ma, sa'ad da Rifkatu ta yi ciki da mutumin nan ɗaya, wato, kakanmu Ishaku,

11. tun ba ta haifi 'ya'yan ba, balle su yi wani abu mai kyau ko marar kyau–don nufin Allah bisa ga zaɓensa ya tabbata, ba ga aikin lada ba, sai dai ga kiransa–

12. aka ce mata, “Wan zai bauta wa ƙanen.”

13. Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Yakubu na so, Isuwa na ƙi.”

14. To, me kuma za mu ce? Allah ya yi rashin adalci ke nan? a'a, ko kusa!

15. Domin ya ce wa Musa, “Wanda zan yi wa jinƙai, zan yi masa jinƙan, wanda zan nuna wa tausayi kuwa, zan nuna masa tausayin.”

16. Ashe kuwa, abin bai danganta ga nufin mutum ko himma tasa ba, sai dai ga jinƙan Allah.

17. Don a Nassi an ce da Fir'auna, “Na girmama ka ne musamman, domin in nuna ikona a kanka, domin kuma a sanar da sunana a duniya duka.”

Rom 9