Rom 11:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. To, ina tambaya. Wato, Allah ya juya wa jama'arsa baya ke nan? A'a, ko kusa! Ai, ni ma da kaina Ba'isra'ile ne, zuriyar Ibrahim, na kabilar Biliyaminu.

2. Ko kaɗan, Allah bai juya wa jama'arsa da ya zaɓa tun dā baya ba. Ko ba ku san abin da Nassi ya faɗa ba ne, a game da Iliya? Yadda ya kai kuka ga Allah, a kan Isra'ila, ya ce,

3. “Ya Ubangiji, sun karkashe annabawanka, sun rurrushe bagadanka na hadaya. Ni kaɗai ne na ragu, suna kuwa neman raina.”

4. Amma me Allah ya amsa masa? Cewa ya yi, “Na keɓe wa kaina mutum dubu bakwai waɗanda ba su taɓa durƙusa wa Ba'al ba.”

5. Haka ma a wannan zamani akwai ragowa, waɗanda aka zaɓa saboda alherinsa.

6. In kuwa na alheri ne, ba sauran cewa ya dogara ga aikin lada ke nan. In ba haka ba, ashe, alheri ba alheri ba ne kuma.

Rom 11