Neh 7:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sa'ad da aka gina garun, aka sa ƙofofinsa, aka kuma sa matsaran ƙofofi, da mawaƙa, da Lawiyawa,

2. sai na ba ɗan'uwana, Hanani, da Hananiya, shugaban kagara, aikin riƙon Urushalima. Shi Hananiya mai aminci ne, mai tsoron Allah, fiye da sauran mutane.

3. Sa'an nan na ce musu, kada su buɗe ƙofofin Urushalima da sassafe, sai rana ta cira sosai, su kuma kulle ƙofofin da ƙarfe kafin matsara su tashi wajen faɗuwar rana. Su samo matsara daga mazaunan Urushalima, su sa su tsaye a muhimman wurare, waɗansunsu kuma suna zaga gidaje.

4. Birnin yana da faɗi da girma, amma mutanen da suke ciki kaɗan ne, ba a kuma gina gidaje ba tukuna.

5. Allahna kuwa ya sa a zuciyata in tara manya da shugabanni, da sauran jama'a don a rubuta su bisa ga asalinsu. Na sami littafin asali na waɗanda suka fara komowa. Ga abin da na tarar aka rubuta ciki.

26-38. Mutanen da kakanninsu suka zauna a waɗannan garuruwa, su ma sun komo daga zaman talala.Baitalami da Netofa, ɗari da tamanin da takwasAnatot, ɗari da ashirin da takwasAzmawet, arba'in da biyuKiriyat-yeyarim da Kefira, da Biyerot, ɗari bakwai da arba'in da ukuRama da Geba, ɗari shida da ashirin da ɗayaMikmash, ɗari da ashirin da biyuBetel da Ai, ɗari da ashirin da ukuDa wani Nebo, hamsin da biyuDa wani Elam, dubu da ɗari biyu da hamsin da huɗu (1,254)Harim, ɗari uku da ashirinYariko, ɗari uku da arba'in da biyarLod, da Hadid, da Ono, ɗari bakwai da ashirin da ɗayaSenaya, dubu uku da ɗari tara da talatin (3,930)

39-42. Ga lissafin iyalin firistoci da suka komo daga zaman talala.Yedaiya, na zuriyar Yeshuwa, ɗari tara da saba'in da ukuImmer, dubu ɗaya da hamsin da biyu (1,052)Fashur, dubu da ɗari biyu da arba'in da bakwai (1,247)Harim, dubu ɗaya da goma sha bakwai (1,017)

46-56. Ma'aikatan Haikali da suka komo daga zaman talala, su neZuriyar Ziha, da Hasufa, da Tabbawot,Keros, da Siyaha, da Fadon,Lebana, da Hagaba, da Shamlai,Hanan, da Giddel, da Gahar,Rewaiya, da Rezin, da Nekoda,Gazam, da Uzza, da Faseya,Besai, da Me'uniyawa, da Nefushiyawa,Bakbuk, da Hakufa, da Harkur,Bazlut, da Mehida, da Harsha,Barkos, da Sisera, da Tema,Neziya, da Hatifa.

Neh 7