2. Gama ba su taryi jama'ar Isra'ila da abinci da abin sha ba, amma suka yi ijara da Bal'amu ya zo ya la'anta musu su, amma Allahnmu ya juyar da la'anar ta zama albarka.
3. Da mutane suka ji dokokin, sai suka ware dukan waɗanda suke ba Isra'ilawa ba.
4. Kafin wannan lokaci Eliyashib, firist, wanda aka sa shi shugaban ɗakunan ajiya na Haikalin Allahnmu, wanda yake da dangantaka da Tobiya,
5. ya shirya wa Tobiya babban ɗaki inda dā aka ajiye hadaya ta gari, da turare, da tasoshi, da zakar hatsi, da ruwan inabi, da mai, waɗanda aka umarta a ba Lawiyawa, da mawaƙa, da masu tsaron ƙofofi, da inda aka ajiye sadakokin da ake ba firistoci.
6. Ba na nan a Urushalima sa'ad da wannan abu ya faru, gama a shekara ta talatin da biyu ta sarautar Artashate, Sarkin Babila, na tafi wurin sarki. Daga baya sarki ya ba ni izini in koma.
7. Da na komo Urushalima, sai na ga mugun abin da Eliyashib ya yi domin Tobiya, yadda ya shirya masa ɗaki a filin Haikalin Allah.
8. Sai na husata ƙwarai, na fitar da kayan ɗakin Tobiya a waje.
9. Sai na umarta, suka kuwa tsarkake ɗakunan, sa'an nan na mayar da tasoshin Haikalin Allah, da hadaya ta gari, turare a ciki.
10. Na kuma iske ba a ba Lawiyawa rabonsu ba. Saboda wannan Lawiyawa da mawaƙa masu hidima suka watse zuwa gonakinsu.
11. Sai na yi wa shugabanni faɗa, na ce, “Me ya sa aka ƙi kula da Haikalin Allah?” Sa'an nan na tara Lawiyawa da mawaƙa, na sa su a wuraren aikinsu.
12. Sai dukan mutanen Yahuza suka kawo zakar hatsi, da ta ruwan inabi, da ta mai, a ɗakunan ajiya.
13. Sai na sa Shelemiya, firist, da Zadok, magatakarda, da Fedaiya daga cikin Lawiyawa su zama masu lura da ɗakunan ajiya. Na kuma sa Hanan ɗan Zakkur, jikan Mattaniya ya yi aiki tare da su, gama su amintattu ne. Aikinsu shi ne su raba wa 'yan'uwansu abin da aka kawo.
14. “Ka tuna da ni, ya Allahna, saboda wannan. Kada ka manta da ayyukan kirki da na yi a Haikalin Allah da kuma na hidimarsa.”
15. A kwanakin nan na ga mutane a Yahuza suna matse ruwan inabi, suna labta wa jakunansu buhunan hatsi, da ruwan inabi, da 'ya'yan inabi, da ɓaure, da kaya iri iri, suna kawo su cikin Urushalima a ran Asabar. Sai na yi musu faɗa a kan sayar da abinci a wannan rana.
16. Mutanen Taya da suke zaune a birnin sukan kawo kifi da kaya iri iri, su sayar wa mutanen Yahuza a Urushalima a ranar Asabar.
17. Sai na tsauta wa manyan mutanen Yahuza, na ce musu, “Wane irin mugun abu ne kuke yi haka, kuna ɓata ranar Asabar?
18. Ashe, ba haka kakanninku suka yi ba, har wannan ya sa Allahnmu ya kawo mana masifa, mu da dukan birnin? Duk da haka kuna ƙara kawo wa Isra'ila hasala saboda kuna ɓata ranar Asabar.”