Neh 12:2-7-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2-7. Amariya, da Malluki, da Hattush,Shekaniya, da Rehum, da Meremot,Iddo, da Ginneton, da Abaija,Miyamin, da Mawadiya, da Bilga,Shemaiya, da Yoyarib, da Yedaiya,Sallai, da Amok, da Halkiya, da Yedaiya.Waɗannan su ne shugabannin firistoci da 'yan'uwansu a zamanin Yeshuwa.

22. A zamanin Eliyashib, da Yoyada, da Yohenan, da Yadduwa, Lawiyawa, har zuwa zamanin mulkin Dariyus, mutumin Farisa, aka rubuta shugabannin gidajen kakannin Lawiyawa da firistoci.

23. Aka kuma rubuta shugabannin gidajen kakannin zuriyar Lawi a tarihi, har zuwa zamanin Yohenan ɗan Eliyashib.

24. Shugabannin Lawiyawa kuwa, su ne Hashabiya, da Sherebiya, da Yeshuwa, da Kadmiyel. 'Yan'uwansu suna tsaye kusa da su daki daki domin su yi yabo, su yi godiya kamar yadda Dawuda mutumin Allah ya umarta.

25. Mattaniya, da Bakbukiya, da Obadiya, da Meshullam, da Talmon, da Akkub su ne masu tsaron ƙofofi, suna tsaron ɗakunan ajiya na wajen ƙofofi.

Neh 12