19. Masu tsaron ƙofofi kuma su ne Akkub, da Talmon, da 'yan'uwansu, su ɗari da saba'in da biyu ne.
20. Sauran jama'ar Isra'ila kuwa, da firistoci, da Lawiyawa suka zauna a dukan garuruwan Yahuza, kowa ya zauna a gādonsa.
21. Amma ma'aikatan Haikali suka zauna a Ofel. Ziha da Gishfa, su ne shugabannin ma'aikatan Haikali.
22. Shugaban Lawiyawan da yake a Urushalima, shi ne Uzzi ɗan Bani, jīkan Hashabiya. Sauran kakanninsa su ne Mattaniya, ɗan Mika daga zuriyar Asaf. Su ne mawaƙa a Haikalin Allah.
23. Sarki ya yi wa shugabannin mawaƙa umarni da ƙarfi a kan abin da za su yi kowace rana.
24. Fetahiya ɗan Meshezabel, daga zuriyar Zera na kabilar Yahuza, shi ne wakilin sarki a kan dukan abin da ya shafi jama'a.