Gama jama'ar Isra'ila da Lawiyawa za su kawo sadakoki na hatsi,da na ruwan inabi, da na mai, a ɗakin ajiya inda tasoshin Haikali suke, da gaban firistocin da suke hidima, da masu tsaron ƙofofi, da mawaƙa.“Ba za mu ƙyale Haikalin Allahnmu ba.”