Neh 11:14-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Tare da 'yan'uwansu, su ɗari da ashirin da takwas ne gwarzayen sojoji ne. Shugabansu shi ne Zabdiyel ɗan Haggedolim.

15. Na wajen Lawiyawa kuwa su ne Shemaiya ɗan Hasshub, jīkan Azrikam. Sauran kakanninsa su ne Hashabiya, da Bunni,

16. da Shabbetai, da Yozabad, ɗaya daga cikin manyan shugabanni na Lawiyawa, waɗanda suke lura da kewayen Haikalin Allah.

17. Da kuma Mattaniya ɗan Mika, jīkan Zikri, zuriyar Asaf, shi ne shugaba na farko na mawaƙan addu'a ta godiya. Bakbukiya, shi ne mataimakin Mattaniya. Ga kuma Obadiya ɗan Shemaiya, jīkan zuriyar Galal, zuriyar Yedutun.

18. Dukan Lawiyawa da suke a tsattsarkan birni su ɗari biyu da tamanin da huɗu ne.

19. Masu tsaron ƙofofi kuma su ne Akkub, da Talmon, da 'yan'uwansu, su ɗari da saba'in da biyu ne.

20. Sauran jama'ar Isra'ila kuwa, da firistoci, da Lawiyawa suka zauna a dukan garuruwan Yahuza, kowa ya zauna a gādonsa.

21. Amma ma'aikatan Haikali suka zauna a Ofel. Ziha da Gishfa, su ne shugabannin ma'aikatan Haikali.

22. Shugaban Lawiyawan da yake a Urushalima, shi ne Uzzi ɗan Bani, jīkan Hashabiya. Sauran kakanninsa su ne Mattaniya, ɗan Mika daga zuriyar Asaf. Su ne mawaƙa a Haikalin Allah.

23. Sarki ya yi wa shugabannin mawaƙa umarni da ƙarfi a kan abin da za su yi kowace rana.

Neh 11