Mat 7:6-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. “Kada ku ba karnuka abin da yake tsattsarka. Kada kuma ku jefa wa alhanzir lu'ulu'unku, don kada su tattake su, su juyo su kyakketa ku.”

7. “Ku yi ta roƙo, za a ba ku. Ku yi ta nema, za ku samu. Ku yi ta ƙwanƙwasawa, za a kuwa buɗe muku.

8. Duk wanda ya roƙa, akan ba shi, mai nema yana tare da samu. Wanda ya ƙwanƙwasa kuma za a buɗe masa.

9. To, wane ne a cikinku, ɗansa zai roƙe shi gurasa, ya ba shi dutse?

10. Ko kuwa ya roƙe shi kifi, ya ba shi maciji?

11. To, ku da kuke mugaye ma, kuka san yadda za ku ba 'ya'yanku kyautar kyawawan abubuwa, balle Ubanku na Sama da zai ba da abubuwan alheri ga masu roƙonsa?

12. Saboda haka duk abin da kuke so mutane su yi muku, ku ma sai ku yi musu, domin wannan shi ne Attaura da koyarwar annabawa.”

13. “Ku shiga ta ƙunƙuntar ƙofa, gama ƙofa zuwa hallaka faffaɗa ce, hanyarta mai sauƙin bi ce, masu shiga ta cikinta suna da yawa.

14. Domin kuwa ƙofar zuwa rai ƙunƙunta ce, hanyarta mai wuyar bi ce, masu samunta kuwa kaɗan ne.”

15. “Ku kula da annabawan ƙarya, waɗanda sukan zo muku da siffar tumaki, amma a zuci kyarketai ne masu ƙāwa.

16. Za ku gane su ta irin aikinsu. A iya ciran inabi a jikin ƙaya, ko kuwa ɓaure a jikin sarƙaƙƙiya?

17. Haka kowane itacen kirki yakan haifi kyawawan 'ya'ya. Mummunan itace kuwa yakan haifi munanan 'ya'ya.

18. Kyakkyawan itace ba dama ya haifi munanan 'ya'ya. Haka kuma mummunan itace ba dama ya haifi kyawawan 'ya'ya.

19. Duk itacen da ba ya 'ya'ya masu kyau, sai a sare shi a jefa a wuta.

20. Don haka, da irin aikinsu za a gane su.”

21. “Ba duk mai ce mini, ‘Ya Ubangiji, ya Ubangiji,’ ne zai shiga Mulkin Sama ba, sai dai wanda ya yi abin da Ubana da yake cikin Sama yake so.

22. A ranar nan da yawa za su ce mini, ‘Ya Ubangiji, ya Ubangiji, ashe, ba mu yi annabci da sunanka ba? Ba mu fitar da aljannu da sunanka ba? Ba mu kuma yi ayyukan al'ajabi masu yawa da sunanka ba?’

23. Sa'an nan zan ce musu, ‘Ni ban taɓa saninku ba. Ku rabu da ni, ku masu yin mugun aiki.’ ”

Mat 7