Mat 5:46-48 Littafi Mai Tsarki (HAU)

46. In masoyanku kawai kuke ƙauna, wane lada ne da ku? Ashe, ko masu karɓar haraji ma ba haka suke yi ba?

47. In kuwa 'yan'uwanku kaɗai kuke gayarwa, me kuka yi fiye da waɗansu? Ashe, ko al'ummai ma ba haka suke yi ba?

48. Saboda haka sai ku zama cikakku, kamar yadda Ubanku na Sama take cikakke.”

Mat 5