Mat 21:21-36 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Yesu ya amsa musu ya ce, “Hakika, ina gaya muku, in dai kuna da bangaskiya, ba tare da wata shakka ba, ba abin da aka yi wa ɓauren nan kaɗai za ku yi ba, har ma in kun ce wa dutsen nan, ‘Ka ciru, ka faɗa teku,’ sai kuwa ya auku.

22. Kome kuka roƙa da addu'a, in dai kuna da bangaskiya, za ku samu.”

23. Ya shiga Haikali yana cikin koyarwa, sai manyan firistoci da shugabannin jama'a suka zo wurinsa, suka ce, “Da wane izini kake yin abubuwan nan, wa ya ba ka izinin?”

24. Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ni ma zan yi muku wata tambaya. In kun ba ni amsa, ni ma sai in gaya muku ko da wane izini nake yin abubuwan nan.

25. To, baftismar da Yahaya ya yi, daga ina take? Daga Sama take, ko kuwa ta mutum ce?” Sai suka yi ta muhawwara da juna, suna cewa, “In muka ce, ‘Daga Sama take,’ sai ya ce mana, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’

26. In kuwa muka ce, ‘Ta mutum ce,’ ai, muna jin tsoron jama'a, don duk kowa ya ɗauki Yahaya a kan annabi ne.”

27. Sai suka amsa wa Yesu suka ce, “Ba mu sani ba.” Shi kuma ya ce musu, “Haka ni kuma ba zan faɗa muku ko da wane izini nake yin abubuwan nan ba.”

28. “To, me kuka gani? An yi wani mutun mai 'ya'ya biyu maza. Ya je wurin na farkon, ya ce, ‘Ɗana, yau je ka ka yi aiki a garkar inabi.’

29. Sai ya ce, ‘Na ƙi.’ Amma daga baya sai ya tuba, ya tafi.

30. Sai ya je gun na biyun ya faɗa masa haka. Shi kuwa ya amsa ya ce, ‘To, za ni, baba,’ amma bai je ba.

31. To, wane ne a cikin su biyun ya yi abin da ubansu yake so?” Sai suka ce, “Na farkon.” Yesu ya ce musu, “Hakika, ina gaya muku, masu karɓar haraji da karuwai suna riga ku shiga Mulkin Allah.

32. Ga shi, Yahaya ya zo ya bayyana muku hanyar adalci, ba ku gaskata shi ba. Amma masu karɓar haraji da karuwai sun gaskata shi, duk da ganin haka kuma, daga baya ba ku tuba kun gaskata shi ba.”

33. “To, ga kuma wani misali. An yi wani maigida da ya yi garkar inabi, ya shinge ta, ya haƙa ramin matse inabi a ciki, ya kuma gina wata 'yar hasumiyar tsaro. Ya ba waɗansu manoma sufurin garkar, sa'an nan ya tafi wata ƙasa.

34. Da kakar inabi ta kusa, sai ya aiki bayinsa wurin manoman nan su karɓo masa gallar garkar.

35. Manoman kuwa suka kama bayinsa, suka yi wa ɗaya dūka, suka kashe ɗaya, suka kuma jajjefi ɗaya.

36. Har wa yau ya sāke aiken waɗansu bayi fiye da na dā, suka kuma yi musu haka.

Mat 21