Mat 21:12-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Sai Yesu ya shiga Haikalin ya kakkori dukkan masu saye da sayarwa a ciki, ya birkice teburorin 'yan canjin kuɗi da kujerun masu sayar da tattabarai.

13. Ya ce musu, “A rubuce yake cewa, ‘Za a kira gidana ɗakin addu'a,’ amma ku kun maishe shi kogon 'yan fashi.”

14. Sai makafi da guragu suka zo wurinsa a Haikalin, ya kuwa warkar da su.

15. Amma manyan firistoci da malaman Attaura suka ga abubuwan al'ajabi da ya yi, har yara suna sowa a Haikalin suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda!” sai suka ji haushi.

16. Suka ce masa, “Kana jin abin da waɗannan suke faɗa?” Yesu kuwa ya ce musu, “I. Amma ba ku taɓa karantawa ba cewa,‘Kai ne ka shiryar da 'yan yara da masu shan mama su yabe ka’?”

17. Sai ya bar su, ya fita daga birnin, ya tafi Betanya, ya sauka a can.

18. Kashegari da sassafe yana komowa birni, sai ya ji yunwa.

19. Da ya ga wani ɓaure a gefen hanya, ya je wurin, amma bai sami kome ba, sai ganye kawai. Sai ya ce wa ɓauren, “Kada ka ƙara yin 'ya'ya har abada!” Nan take ɓauren ya bushe.

20. Da almajiran suka ga haka, suka yi mamaki suka ce, “Yaya ɓauren nan ya bushe haka nan da nan?”

21. Yesu ya amsa musu ya ce, “Hakika, ina gaya muku, in dai kuna da bangaskiya, ba tare da wata shakka ba, ba abin da aka yi wa ɓauren nan kaɗai za ku yi ba, har ma in kun ce wa dutsen nan, ‘Ka ciru, ka faɗa teku,’ sai kuwa ya auku.

22. Kome kuka roƙa da addu'a, in dai kuna da bangaskiya, za ku samu.”

23. Ya shiga Haikali yana cikin koyarwa, sai manyan firistoci da shugabannin jama'a suka zo wurinsa, suka ce, “Da wane izini kake yin abubuwan nan, wa ya ba ka izinin?”

24. Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ni ma zan yi muku wata tambaya. In kun ba ni amsa, ni ma sai in gaya muku ko da wane izini nake yin abubuwan nan.

25. To, baftismar da Yahaya ya yi, daga ina take? Daga Sama take, ko kuwa ta mutum ce?” Sai suka yi ta muhawwara da juna, suna cewa, “In muka ce, ‘Daga Sama take,’ sai ya ce mana, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’

26. In kuwa muka ce, ‘Ta mutum ce,’ ai, muna jin tsoron jama'a, don duk kowa ya ɗauki Yahaya a kan annabi ne.”

27. Sai suka amsa wa Yesu suka ce, “Ba mu sani ba.” Shi kuma ya ce musu, “Haka ni kuma ba zan faɗa muku ko da wane izini nake yin abubuwan nan ba.”

Mat 21