Mat 15:1-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Waɗansu Farisiyawa da malaman Attaura suka zo wurin Yesu daga Urushalima, suka ce,

2. “Don me almajiranka suke keta al'adun shugabanni? Domin ba sa wanke hannu kafin su ci abinci.”

3. Sai ya amsa musu ya ce, “Ku kuma don me kuke keta umarnin Allah saboda al'adunku?

4. Domin Allah ya yi umarni ya ce, ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,’ kuma ‘Wanda ya zagi ubansa ko uwa tasa lalle a kashe shi.’

5. Amma ku kukan ce, ‘Kowa ya ce wa ubansa ko uwa tasa, “Duk abin da dā za ku samu a gare ni an ba Allah,” to, ba lalle ya girmama ubansa ba ke nan.’

6. Wato, saboda al'adunku kun bazanta Maganar Allah.

7. Ku munafukai! Daidai ne Ishaya ya yi annabci a kanku, da ya ce,

8. ‘Al'ummar nan a baka kawai suke girmama ni,Amma a zuci nesa suke da ni.

9. A banza suke bauta mini,Don ka'idodin da suke koyarwa umarnin ɗan adam ne.’ ”

10. Ya kira taro ya ce musu, “Ku saurara, ku fahimta.

11. Ba abin da yake shiga mutum ta baka ne yake ƙazanta shi ba, abin da yake fita ta baka yake ƙazanta mutum.”

12. Sai almajiran suka zo suka ce masa, “Ka san Farisiyawa sun ji haushi da suka ji maganan nan?”

13. Ya amsa ya ce, “Duk dashen da ba Ubana da yake Sama ne ya dasa ba, za a tumɓuke shi.

14. Ƙyale su kawai, makafin jagora ne. In kuwa makaho ya yi wa makaho jagora, ai, duk biyu sai su faɗa a rami.”

15. Amma Bitrus ya ce masa, “A yi mana fassarar misalin nan.”

16. Yesu ya ce, “Ku ma, ashe, har yanzu ba ku fahimta?

17. Ashe, ba ku gane ba, kome ya shiga mutum ta baka, cikinsa ya shiga, ta haka kuma zai fice?

18. Amma abin da ya fito ta baka, daga zuci yake, shi ne kuwa yake ƙazantar da mutum.

Mat 15