7. Sai ku koya wa 'ya'yanku su da himma. Za ku haddace su sa'ad da kuke zaune a gida, da sa'ad da kuke tafiya, da sa'ad da kuke kwance, da sa'ad da kuka tashi.
8. Za ku ɗaura su a hannunku da goshinku don alama.
9. Za ku kuma rubuta su a madogaran ƙofofin gidajenku, da ƙofofinku.”
10. “Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya kai ku ƙasar da ya rantse wa kakanninku Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, zai ba ku manyan birane masu kyau waɗanda ba ku ne kuka gina ba,
11. da gidaje cike da abubuwa masu kyau waɗanda ba ku ne kuka cika su ba, da rijiyoyi waɗanda ba ku ne kuka haƙa ba, da gonakin inabi da itatuwan zaitun waɗanda ba ku ne kuka dasa ba. Sa'ad da kuka ci, kuka ƙoshi,
12. to, kada ku manta da Ubangiji wanda ya fito da ku daga ƙasar Masar, daga gidan bauta.
13. Sai ku ji tsoron Ubangiji Allahnku. Shi ne za ku bauta masa, ku rantse da sunansa.
14. Kada ku bi waɗansu alloli na al'umman da suke kewaye da ku,
15. gama Ubangiji Allahnku wanda yake zaune a tsakiyarku, mai kishi ne, don kada Ubangiji Allahnku ya husata, ya shafe ku daga duniya.
16. “Kada ku gwada Ubangiji Allahnku kamar yadda kuka yi a Masaha.
17. Sai ku himmantu ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, da farillansa, da dokokinsa waɗanda ya umarce ku da su.
18. Sai ku yi abin da yake daidai, da abin da yake mai kyau a gaban Ubangiji saboda lafiyarku, domin kuma ku shiga ku mallaki ƙasa mai kyau wadda Ubangiji ya rantse zai ba kakanninku.