9. “Sai ku lura, ku kiyaye kanku sosai, don kada ku manta da abubuwan da kuka gani da idonku kada kuma su fita a ranku dukan kwanakinku. Ku sanar wa 'ya'yanku da jikokinku da su,
10. da yadda kuma a waccan rana kuka tsaya a gaban Ubangiji Allahnku a Horeb, sa'ad da Ubangiji ya ce mini, ‘Ka tattara mini jama'a domin su ji maganata, su koyi tsorona dukan kwanakinsu a duniya, su kuma koya wa 'ya'yansu.’
11. “Sai kuka matso kusa, kuka tsaya a gindin dutsen sa'ad da dutsten yake cin wuta har zuwa sararin sama, ga kuma girgije baƙi ƙirin yana rufe da dutsen.
12. Ubangiji kuwa ya yi magana da ku ta tsakiyar wuta. Kuka ji hurcin kalmomin, amma ba ku ga siffar kome ba, sai dai murya kaɗai kuka ji.
13. Shi ne ya hurta muku shari'ar da ya umarce ku ku kiyaye, wato dokokin nan goma. Ya rubuta su a allunan dutse guda biyu.
14. Duk da haka Ubangiji ya umarce ni in koya muku dokokin da farillan don ku aikata su a ƙasar da kuke hayewa zuwa ciki don ku mallake ta.”
15. “Domin haka, sai ku kula da kanku sosai, gama ba ku ga siffar kome ba sa'ad da Ubangiji Allahnku ya yi magana da ku a Horeb ta tsakiyar wuta.
16. don kada ku yi mugunta, ku sassaƙa wa kanku wata siffar kowane abu, ko siffar mace ko ta namiji,