M. Sh 17:7-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Sai shaidun su fara jifansa sa'an nan sauran jama'a su jajjefe shi. Ta haka za a kawar da mugunta daga cikinsu.

8. “Idan aka kawo muku shari'a mai wuyar yankewa a ɗakin shari'arku, ko ta kisankai ce, ko ta jayayya ce, ko ta cin mutunci ce, ko kowace irin shari'a mai wuyar yankewa, sai ku tashi, ku tafi wurin da Ubangiji Allahnku zai zaɓa.

9. Za ku kai maganar wurin Lawiyawan da suke firistoci, ko kuma a wurin alƙalin da yake aiki a lokacin. Za ku tambaye su, za su faɗa muku yadda za a yanke shari'a.

10. Sai ku yanke shari'ar yadda suka faɗa muku daga wurin da Ubangiji ya zaɓa. Ku lura fa, ku yi yadda suka faɗa muku.

11. Dole ne ku yi yadda suka koya muku, da yadda suka yanke shari'ar. Kada ku kauce dama ko hagu daga maganar da suka faɗa muku.

12. Duk wanda ya yi izgili, ya ƙi yin biyayya da firist wanda yake a can, yana yi wa Ubangiji Allahnku hidima, ko kuma ya ƙi yi wa alƙalin biyayya, to, lalle sai a kashe wannan mutum. Ta haka za ku kawar da mugunta daga cikin Isra'ilawa.

13. Sa'an nan duk jama'a za su ji, su kuwa ji tsoro. Ba za su ƙara yin izgilanci ba kuma.”

14. “Sa'ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku don ku mallake ta, ku zauna a ciki, sa'an nan ku yi tunanin naɗa wa kanku sarki, kamar al'umman da suke kewaye da ku,

15. to, kwā iya naɗa wa kanku sarki wanda Ubangiji Allahnku ya zaɓa. Sai ku naɗa wa kanku sarki daga cikin jama'arku. Kada ku naɗa wa kanku baƙo wanda ba ɗan'uwanku ba.

M. Sh 17