2. “Ka umarci jama'ar Isra'ila, ka ce su ba Lawiyawa biranen da za su zauna a ciki daga cikin gādonsu, za su kuma ba Lawiyawa hurumi kewaye da biranen.
3. Biranen za su zama nasu, inda za su zauna, hurumi kuwa domin shanunsu da sauran dukan dabbobinsu.
4. Girman hurumin da za su ba Lawiyawa kewaye da biranen zai zama mai fāɗin kamu dubu kewaye da garun birnin.
5. A bayan birnin za a auna kamu dubu biyu a wajen gabas, kamu dubu biyu a wajen kudu, kamu dubu biyu a wajen yamma, kamu dubu biyu a wajen arewa. Wannan zai zama hurumin mutanen birnin. Birnin kuwa zai kasance a tsakiya.
6. A cikin biranen da za a ba Lawiyawa, shida su zama na mafaka, inda za a yarda wa mai kisankai ya gudu zuwa can. Banda biranen mafaka guda shida, za a kuma ba su birane arba'in da biyu.
7. Wato dukan biranen da za a ba Lawiyawa guda arba'in da takwas ne tare da huruminsu.
8. Isra'ilawa za su ba Lawiyawa biranen nan bisa ga girman mallakarsu. Manyan kabilai za su ba su birane da yawa, amma ƙananan kabilai za su ba su birane kaɗan.”
9. Ubangiji kuwa ya faɗa wa Musa,
10. ya ce wa jama'ar Isra'ila, “Sa'ad da kuka haye Urdun zuwa cikin ƙasar Kan'ana,
11. sai ku keɓe wa kanku biranen mafaka domin wanda ya yi kisankai da kuskure, ba da niyya ba, ya gudu zuwa can.
12. Biranen za su zamar muku mafaka daga hannun mai bin hakkin jini, don kada a kashe mai kisankai tun bai riga ya tsaya a gaban shari'a ba.
13. Sai ku zaɓi birane shida.
14. Biranen mafaka uku a hayin gabashin Urdun, birane uku kuma a ƙasar Kan'ana.
15. Waɗannan birane shida za su zama wuraren mafaka ga jama'ar Isra'ila, da baƙi, da baren da yake zaune tare da su, domin duk wanda ya kashe wani ba da niyya ba, ya tsere zuwa can.
16. “Amma idan wani ya bugi wani da makami na ƙarfe har ya mutu, ya yi kisankai, sai a kashe shi.
17. Idan kuwa ya jefe shi da dutsen da ya isa a yi kisankai da shi, har ya mutu, ya yi kisankai ke nan, to, sai a kashe shi.
18. Idan kuwa ya buge shi da makami na itace da ya isa a yi kisankai da shi, har kuwa ya mutu, ya yi kisankai ka nan, sai a kashe shi.