19. Sai mai bin hakkin jinin ya kashe mai kisankan sa'ad da ya iske shi.
20. “Idan saboda ƙiyayya ya laɓe, ya soke shi, ko ya jefe shi har ya mutu,
21. ko kuma saboda ƙiyayya ya naushe shi da hannu har ya mutu, sai a kashe shi, gama ya yi kisankai ke nan. Wanda yake bin hakkin jinin, zai kashe wanda ya yi kisankai sa'ad da ya iske shi.
22. “Amma idan bisa ga tsautsayi ya soke shi, ba don ƙiyayya ba, ko kuwa idan ya jefe shi da kowane abu, ba a laɓe ba,
23. ko ya jefe shi da dutsen da ya isa a kashe mutum da shi, ba da saninsa ba, shi kuwa ba maƙiyinsa ba ne, bai kuwa yi niyya ya cuce shi ba, amma ga shi kuwa, ya kashe shi,
24. to, sai taron jama'a su hukunta tsakanin mai kisankan da mai bin hakkin jinin bisa ga waɗannan ka'idodi.
25. Taron jama'a za su ceci mai kisankan daga hannun mai bin hakkin jinin. Su komar da shi a birnin mafaka inda ya je neman mafaka. Zai zauna can sai lokacin da babban firist da aka keɓe da tsattsarkan mai ya rasu.
26. Amma idan a wani lokaci mai kisankan ya fita kan iyakar birnin mafaka inda yake,
27. idan mai bin hakkin jinin ya same shi a bayan iyakar birnin, ya kashe shi, bai yi laifi ba.
28. Gama dole ne mai kisankan ya zauna cikin birnin mafaka inda yake, sai bayan rasuwar babban firist. Bayan rasuwar babban firist, mai kisankan yana iya komawa ƙasarsa.”
29. “Waɗannan ka'idodi sun shafe ku da zuriyarku a duk inda kuke.
30. Duk wanda ya yi kisankai sai a kashe shi bisa ga shaidar shaidu, amma saboda shaidar mutum ɗaya ba za a kashe mutum ba.
31. Kada ku karɓi fansa don ran wanda ya yi kisankai, dole ne a kashe shi.
32. Haka nan kuma kada ku karɓi fansa saboda wanda ya tsere zuwa birnin mafaka don ya koma ya zauna gidansa tun babban firist bai rasu ba.
33. Saboda haka kada ku ƙazantar da ƙasar da kuke zaune a ciki, gama jini yakan ƙazantar da ƙasa. Ba wata kafara da za a yi don ƙasar da aka zubar da jini a cikinta, sai dai da jinin wanda ya zubar da jinin.
34. Kada ku ƙazantar da ƙasar da kuke zaune a ciki, wadda ni kuma nake zaune a ciki, gama ni Ubangiji ina zaune a tsakiyar jama'ar Isra'ila.”