L. Kid 28:19-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimai biyu, da rago ɗaya, da 'yan raguna bakwai bana ɗaya ɗaya ga Ubangiji. Dukansu su zama marasa lahani.

20. Za a kuma miƙa hadaya ta gari tare da dabbobin, da lallausan gari wanda aka kwaɓa da man zaitun, gari humushi uku na garwa tare da kowane bijimi, da gari humushi biyu tare da kowane rago,

21. gari humushi ɗaya tare da kowane ɗan rago.

22. Za a miƙa bunsuru guda don yin hadaya don zunubi, domin yin kafara.

23. Za a miƙa waɗannan hadayu banda hadaya ta ƙonawa wadda akan miƙa kowace safiya.

24. Haka za a miƙa abinci na hadaya ta ƙonawa kowace rana har kwana bakwai, domin daɗin ƙanshi ga Ubangiji. Za a kuma riƙa miƙa hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta sha.

25. A rana ta bakwai za a yi tsattsarkan taro, ba za a yi aiki ba.

26. Za a yi tsattsarkan taro a ranar nunan fari, wato idi na mako bakwai lokacin da za a miƙa wa Ubangiji hadaya da sabon hatsi. A ranar ba za a yi aiki ba.

27. Za a miƙa hadaya ta ƙonawa, da 'yan bijimai biyu, da rago ɗaya, da 'yan raguna bakwai bana ɗaya ɗaya don daɗin ƙanshi ga Ubangiji.

28. Za a miƙa hadaya ta gāri tare da dabbobin, da lallausan gari wanda aka kwaɓa da mai, gari humushi uku na garwa, za a miƙa tare da kowane bijimi, humushi biyu na garwa don rago,

29. da humushin garwa don kowane ɗan rago.

L. Kid 28