L. Kid 16:17-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Sa'an nan kowane ɗayanku ya ɗauki farantinsa na ƙona turare, ya zuba turaren wuta a ciki, ya kawo a gaban Ubangiji, wato farantan ƙona turare guda ɗari biyu da hamsin ke nan. Kai kuma da Haruna kowannenku ya kawo nasa faranti.”

18. Sai kowannensu ya ɗauki farantinsa, ya zuba wuta a ciki, sa'an nan ya zuba turaren wuta, suka tsaitsaya a bakin ƙofar alfarwa ta sujada tare da Musa da Haruna.

19. Sai Kora ya tara dukan taron jama'a a bakin alfarwa ta sujada, ya zuga su su tayar wa Musa, da Haruna. Sai ɗaukakar Ubangiji ta bayyana ga dukan taron jama'ar.

20. Ubangiji kuwa ya ce wa Musa da Haruna,

21. “Ku ware kanku daga cikin taron jama'ar nan, ni kuwa in hallaka su nan take.”

22. Sai Musa da Haruna suka fāɗi rubda ciki, suka ce, “Ya Allah, Allahn ruhohin 'yan adam duka, za ka yi fushi da dukan taron jama'a saboda zunubin mutum ɗaya?”

23. Sai Ubangiji ya ce wa Musa,

24. “Ka faɗa wa jama'a su tashi, su nisanci alfarwar Kora, da ta Datan, da ta Abiram.”

25. Musa kuwa ya tashi ya tafi wurin Datan, da Abiram Dattawan Isra'ilawa suka bi Musa.

26. Sai ya ce wa jama'ar, “Ina roƙonku, ku ƙaurace wa alfarwan waɗannan mugayen mutane, kada ku taɓa kowane abu da yake nasu, domin kada a shafe ku saboda zunubansu.”

27. Sai jama'a suka tashi daga inda Kora, da Datan, da Abiram suke zama.Datan da Abiram kuwa suka fito suka tsaya a ƙofar alfarwansu tare da matansu da 'ya'yansu, da 'yan ƙananansu.

28. Sai Musa ya ce, “Da haka za ku sani Ubangiji ne ya aiko ni, in yi waɗannan ayyuka, ba da nufin kaina na yi su ba.

29. Idan mutanen nan sun mutu kamar yadda mutane suke mutuwa, idan abin da yakan sami kowa shi ne ya same su, to, ba Ubangiji ne ya aiko ni ba.

L. Kid 16