Sai Kora ya tara dukan taron jama'a a bakin alfarwa ta sujada, ya zuga su su tayar wa Musa, da Haruna. Sai ɗaukakar Ubangiji ta bayyana ga dukan taron jama'ar.