Sai kowannensu ya ɗauki farantinsa, ya zuba wuta a ciki, sa'an nan ya zuba turaren wuta, suka tsaitsaya a bakin ƙofar alfarwa ta sujada tare da Musa da Haruna.