Josh 8:5-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Da ni da dukan mutanen da suke tare da ni za mu je kusa da birnin. Sa'ad da za su fito don su yi karo da mu kamar dā, za mu gudu daga gare su.

6. Za su kuwa fito su bi mu. Mu kuwa za mu janye su nesa da birnin, gama za su ce, ‘Suna gudunmu kamar dā.’ Haka fa, za mu gudu daga gare su.

7. Ku kuwa ku tashi daga kwanto, ku ci birnin, gama Ubangiji Allahnku zai ba da shi a hannunku.

8. A sa'ad da kuka ci birnin, ku sa wa birnin wuta yadda Ubangiji ya ce. Ku lura fa, da abin da na umarce ku.”

9. Sai Joshuwa ya sallame su, suka tafi inda za su yi kwanto. Suka yi fako tsakanin Betel da Ai, yamma da Ai, amma shi ya kwana tare da jama'a.

10. Joshuwa kuwa ya tashi da sassafe ya tattara mutanen, ya tafi tare da shugabannin Isra'ilawa, suka wuce gaba, suka bi da mutane zuwa Ai.

11. Dukan mayaƙan da suke tare da shi, suka tafi kusa da birnin, suka kafa sansaninsu arewacin Ai. Tsakaninsu da Ai akwai kwari.

Josh 8