13. Mutanensu suka kafa sansaninsu arewa da birnin, sansani na 'yan kwanto kuwa yana yamma da birnin, amma Joshuwa ya kwana a kwarin.
14. A sa'ad da Sarkin Ai ya ga wannan, shi da mutanensa duka, wato mutanen birnin, suka gaggauta, suka tafi da sassafe zuwa gangaren wajen Araba don su gabza yaƙi da Isra'ilawa, amma bai san akwai 'yan kwanto a bayan birnin ba.
15. Sai Joshuwa da mutanensa duka suka nuna kamar an rinjaye su, suka yi ta gudu, suka nufi jeji.
16. Saboda haka aka kira dukan mutanen da suke cikin birnin, su fafare su. Da suka fafari Joshuwa, sai aka janye su nesa da birnin.
17. Ba namijin da ya ragu cikin Ai da bai fita ya fafari Isra'ilawa ba, suka bar birnin a buɗe, suka fafari Isra'ilawa.
18. Ubangiji ya ce wa Joshuwa, “Ka miƙa mashin da yake hannunka wajen Ai, gama zan ba da ita a hannunka.” Sai Joshuwa ya miƙa mashin da yake hannunsa wajen birnin. Nan da nan da ya ɗaga hannunsa
19. 'yan kwanto suka tashi da sauri daga maɓoyansu, suka shiga birnin, suka ci shi, suka yi sauri, suka cuna wa birnin wuta.
20. Da mutanen Ai suka waiga, sai ga hayaƙin birnin ya murtuke zuwa sama, suka rasa ikon da za su gudu gaba ko baya, gama mutanen da suka gudu zuwa jeji, sun juyo kan masu fafararsu.