Josh 8:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji kuma ya ce wa Joshuwa, “Kada ka ji tsoro ko ka firgita. Ka ɗauki mayaƙa duka, ka tashi, ka tafi Ai. Ga shi, na riga na ba da Sarkin Ai da mutanensa, da birninsa, da ƙasarsa a hannunka.

2. Za ka yi wa Ai da sarkinta kamar yadda ka yi wa Yariko da sarkinta, sai dai ganima da dabbobinta ne za ku washe domin kanku. Ku yi kwanto a bayan birnin.”

3. Joshuwa kuwa tare da dukan mayaƙa suka yi shirin tashi zuwa Ai. Sai Joshuwa ya zaɓi jarumawa ƙarfafa dubu talatin (30,000), ya aike su da dad dare.

4. Ya umarce su, ya ce, “Ku tafi, ku yi kwanto a bayan birnin, kada ku yi nisa da birni da yawa, amma dukanku ku kasance da shiri sosai.

5. Da ni da dukan mutanen da suke tare da ni za mu je kusa da birnin. Sa'ad da za su fito don su yi karo da mu kamar dā, za mu gudu daga gare su.

6. Za su kuwa fito su bi mu. Mu kuwa za mu janye su nesa da birnin, gama za su ce, ‘Suna gudunmu kamar dā.’ Haka fa, za mu gudu daga gare su.

Josh 8