Josh 6:20-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Jama'a suka yi ihu, aka busa ƙahoni. Nan da nan da jama'ar suka ji muryar ƙaho, suka yi ihu da babbar murya, sai garun ya rushe tun daga tushenta. Jama'a kuwa suka shiga birnin, kowanne ya nufi inda ya fuskanta sosai, suka ci birnin.

21. Sa'an nan suka hallakar da dukan abin da yake a cikin birnin, da mata da maza, yara da tsofaffi, da shanu da tumaki, da jakai.

22. Sa'an nan Joshuwa ya ce wa mutum biyu ɗin nan da suka leƙo asirin ƙasar, “Tafi gidan karuwar, ku fitar da ita, da dukan waɗanda suke nata kamar yadda kuka rantse mata.”

23. Sai samarin da suka leƙo asirin ƙasar suka shiga, suka fito da Rahab, da mahaifinta, da mahaifiyarta, da 'yan'uwanta, da dukan waɗanda suke nata, suka fito da dukan danginta, suka saukar da su a bayan zangon Isra'ilawa.

24. Suka ƙone birnin da wuta da dukan abin da yake a cikinsa, sai dai azurfa, da zinariya, da kwanonin tagulla, da na baƙin ƙarfe ne, suka ajiye a cikin taskar masujadar Ubangiji.

25. Amma Joshuwa ya bar Rahab da rai, da ita da iyalin mahaifinta, da dukan waɗanda suke nata. Rahab ta yi zamanta wurin Isra'ilawa har wa yau domin ta ɓoye manzannin da Joshuwa ya aika don su leƙo asirin Yariko.

26. A lokacin nan Joshuwa ya yi musu magana da rantsuwa ya ce,“La'ananne ne mutum a gaban UbangijiWanda ya tashi don ya sāke gina birnin nan Yariko.A bakin ɗan farinsa zai kafa tushensa,A bakin autansa kuma zai gina ƙofofinsa.”

27. Ubangiji yana tare da Joshuwa, ya kuwa yi suna cikin dukan ƙasar.

Josh 6