Josh 23:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. An daɗe bayan da Ubangiji ya hutar da Isra'ilawa daga abokan gābansu waɗanda suke kewaye da su. Joshuwa kuwa ya tsufa, shekarunsa sun yi yawa.

2. Sai Joshuwa ya kira Isra'ilawa duka, da dattawansu, da shugabanninsu, da alƙalansu, da jarumawansu, ya ce musu, “Yanzu na tsufa, shekaruna sun yi yawa,

3. kun dai ga abin da Ubangiji Allahnku ya yi da waɗannan al'ummai duka saboda ku, gama Ubangiji Allahnku shi ne wanda ya yi yaƙi dominku.

4. Ga shi kuma, na rarraba wa kabilanku ƙasashen al'umman da suka ragu, da na waɗanda na shafe su tsakanin Urdun da Bahar Rum wajen yamma.

5. Ubangiji Allahnku ne zai sa su gudu a gabanku, ya kore su daga ƙasar. Za ku mallaki ƙasarsu kamar yadda Ubangiji Allahnku ya alkawarta muku.

Josh 23