8. Waɗannan birane da wuraren kiwo nasu su ne jama'ar Isra'ila suka ba Lawiyawa ta hanyar jefa kuri'a kamar yadda Ubangiji ya umarta ta bakin Musa.
9. Daga cikin kabilar Yahuza da kabilar Saminu aka ba zuriyar Haruna waɗannan birane da aka ambata.
10. Zuriyar Haruna tana cikin iyalan Kohatawa waɗanda suke Lawiyawa. Kuri'arsu ce ta fito da farko.
11. Sai aka ba su Kiriyat-arba, wato Hebron, a ƙasar tuddai ta Yahuza tare da wuraren kiwo nata da suke kewaye. Arba shi ne mahaifin Anak.
12. Amma saurukan birnin da ƙauyukansu an ba Kalibu, ɗan Yefunne, su zama mallakarsa.
13. Biranen da aka ba zuriyar Haruna firist ke nan, Hebron tare da wuraren kiwo nata, ita kuwa birnin mafaka ce saboda wanda ya yi kisankai, da Libna tare da wuraren kiwo nata,
14. da Yattir tare da wuraren kiwo nata, da Eshtemowa tare da wuraren kiwo nata,
15. da Holon tare da wuraren kiwo nata, da Debir tare da wuraren kiwo nata,
16. da Ayin tare da wuraren kiwo nata, da Yutta tare da wuraren kiwo nata, da Bet-shemesh tare da wuraren kiwo nata. Birane tara ke nan daga cikin kabilun nan biyu.
17. Daga cikin kabilar Biliyaminu aka ba su birane huɗu, wato Gibeyon tare da wuraren kiwo nata, da Geba tare da wuraren kiwo nata,
18. da Anatot tare da wuraren kiwo nata, da Almon tare da wuraren kiwo nata.
19. Dukan biranen da aka ba firistoci, wato zuriyar Haruna, guda goma sha uku ne tare da wuraren kiwo nasu.
25. Daga cikin rabin kabilar Manassa, aka ba su birane biyu, su ne Ta'anak tare da wuraren kiwo nata, da Bileyam tare da wuraren kiwo nata.